Home / Labarai / NASENI ta tallafa wa magidanta 1,000 da murhun girki na zamani da kayan abinci a Kano

NASENI ta tallafa wa magidanta 1,000 da murhun girki na zamani da kayan abinci a Kano

Hukumar bunƙasa kimiyya da fasahar kere-kere ta kasa (NASENI) ta raba murhunan girki masu amfani da makamashi na zamani, shinkafa, gawayi da sauran kayan tallafi ga iyalai 1,000 a karamar hukumar Sumaila ta Jihar Kano.

An gudanar da rabon tallafin ne a ƙarƙashin kashi na huɗu na shirin hukumar na inganta muhalli mai ɗorewa.

Babban daraktan NASENI, Injiniya Khalil Suleiman Halilu, ya ce shirin na da nufin kusantar da fasahar zamani ga talakawa domin sauƙaƙa rayuwarsu.

Ya bayyana cewa murhunan za su taimaka wajen rage yawan man girki da hayakin da ake fitarwa yayin dafa abinci, tare da rage kuɗaɗen da magidanta ke kashewa a kullum.

Halilu ya bukaci waɗanda suka amfana da tallafin da su kula da kayan, tare da bin ƙa’idojin amfani da su domin samun moriyarsu na dogon lokaci.

Ya kuma jaddada cewa NASENI za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da ke haɗa fasaha da ci gaban al’umma, bisa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope Agenda.

Daraktan ya yaba wa Sanata Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila bisa goyon bayan da ya bayar wajen tabbatar da shirin, tare da godiya ga gwamnatin Kano, hukumomin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya.

A nasa jawabin, Sanata Kawu Sumaila ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa ayyukan raya ƙasa da take gudanarwa a yankin Kano ta Kudu.

Sanatan ya ce ya fi son nuna nasarorin da ya samu ta hanyar ayyukan da aka aiwatar maimakon dogaro da alkawura kawai.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na farfaɗo da wasu ayyukan ban-ruwa da suka daɗe a tsare, ciki har da madatsar ruwan Chalawa Goje da ke Karaye, wadda ya ce ta kwashe kusan shekaru 32 zuwa 34 ba tare da aiki ba.

Ya ƙara da cewa ana kuma gudanar da ayyuka a wasu wuraren ban-ruwa da suka haɗa da na Ƙaramar Hukumar Bunkure da madatsar ruwan Kafinchiri, wadda ya ce ta kwashe kusan shekaru 48 a lalace.

Sanata Kawu Sumaila ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaba Tinubu da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa haɗin kai a siyasance na da muhimmanci wajen kawo ci gaba.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin sun nuna godiyarsu ga gwamnatin tarayya da NASENI, inda suka ce kayan za su taimaka wajen rage musu nauyin kuɗaɗen gudanar da harkokin yau da kullum.