Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta cire sunan dan takarar Gwamnan Kano a NDC, Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo daga cikin jerin ’yan takarar Gwamnan Kano 17 da hukumar ta fitar.
Wannan na cikin sanarwar da INEC ta fitar a ranar Asabar 10 ga Oktobar 2026.
Jerin ya ƙunshi Gashash Mukhtar na AP, Haruna Abdullahi na AA, Sharif Abba na AAC, Ibrahim Ali Amin na ADC da Muhammad Abdullahi na ADP.
Sauran ’yan takarar sun haɗa da Yusuf Abba Kabir na APC, Tijjani Sukairaju Tijjani na APGA, Muhammad Bashir Galadanchi na APM, Tukur Aliyu Malam na APP, Ahmad Furera na BP da Bari Mustapha Bello na DLA.
Haka kuma, jerin ya ƙunshi Santuraki Hamisu na LP, Abdullahi Mustapha na NDP, Abacha Muhammed Sani na PDP, Koguna Nasiru Hassan na PRP, Hussaini Bello Ado na SDP da Nuhu Isa na ZLP.
A cikin jerin sunayen da INEC ta fitar, sunan Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo bai bayyana ba, yayin da Abacha Muhammed Sani yake cikin jerin a matsayin ɗan takarar PDP na Gwamnan Jihar Kano.
Source: Arewa Updates.





