Home / Latest / An yanke wa wata mata hukuncin ɗaurin shekara biyu kan safarar yarinya don lalata da ita

An yanke wa wata mata hukuncin ɗaurin shekara biyu kan safarar yarinya don lalata da ita

Babbar kotun jihar Borno da ke Maiduguri ta yanke wa wata mata mai shekaru 37, Fatima Sanda, hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari bisa laifin kai wata yarinya ’yar shekara 16 ga wasu domin lalata da ita.

Hukumar yaƙi da safarar mutane ta kasa (NAPTIP) ce ta bayyana hakan, inda ta ce kotun ta kuma umarci wadda aka yanke wa hukuncin ta biya yarinyar diyya ta Naira 500,000.

Mai shari’a Aisha M. Ndume ce ta yanke hukuncin, bisa tanadin sashe na 16(1) na dokar hana safarar mutane ta shekarar 2015, wacce aka yi wa gyara.

Wannan hukunci ya zo ne kusan wata guda bayan wata kotun jihar Neja da ke Minna ta yanke wa Hussaini Suleiman, mai shekaru 27, hukuncin ɗaurin shekara bakwai bisa laifin lalata da wata yarinya ’yar shekara takwas.