Home / Latest / APC ta naɗa T-Gwarzo a matsayin darakta janar na yaƙin neman zaɓen Abba da Tinubu a Kano

APC ta naɗa T-Gwarzo a matsayin darakta janar na yaƙin neman zaɓen Abba da Tinubu a Kano

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta naɗa tsohon mataimakin gwamnan jihar kuma tsohon minista, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, a matsayin Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Sanarwar naɗin ta bayyana cewa Gwarzo, wanda aka fi sani da T-Gwarzo, zai jagoranci ayyukan yau da kullum na yaƙin neman zaɓen APC a jihar Kano.

Kwamitin ya ƙunshi mambobi 18, inda aka naɗa Bala Muhammad Gwagwarwa a matsayin mataimakin darakta janar na farko, yayin da Yunusa Adamu Dangwani zai zama mataimakin darakta janar na shiyyar Kano ta Kudu.

Haka kuma, Ali Haruna Abubakar Makoda ne zai kula da shiyyar Kano ta Arewa, yayin da Sanata Abdussalam Abdulkarim, wanda aka fi sani da A.A. Zaura, zai jagoranci shiyyar Kano ta Tsakiya a matsayin mataimakin darakta janar.

A ɓangaren yaɗa manufofin kamfen ɗin, Garba Yusuf Abubakar ne aka naɗa babban mai magana da yawun kwamitin, tare da Sunusi Majidadi Kiru, Musa Iliyasu Kwankwaso, Bashir Sanata da Haj. A’isha Shariff a matsayin sauran masu magana da yawun kamfen ɗin.

Sauran waɗanda ke cikin kwamitin sun haɗa da Dr. Mariya Mahmoud Bunkure, Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Attah, Prof. Aliyu Isa Aliyu, Dr. Kabiru Sani Yakubu, Nana Asmau Jibrin, Aminu Musa Gabasawa, Dr. Hamisu Sadi Ali da Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda aka naɗa a matsayin sakataren kwamitin.

Shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ne ya sanya wa takardar naɗin hannu.

Sanarwar, wadda Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce nan da ’yan kwanaki masu zuwa ne za a sanar da shugabannin sassa daban-daban na kwamitin yaƙin neman zaɓen.