
Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce jam’iyyarsa ta APGA za ta ci gaba da haɗin gwiwa da Shugaba Bola Tinubu wajen neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027.
Soludo ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Abuja, inda ya ce APGA na goyon bayan Tinubu saboda ƙudurinsa na tabbatar da haɗin kan Najeriya, tsaro da wadata ga kowa.
Gwamnan ya ce matakan gyaran tattalin arzikin da Tinubu ya ɗauka suna da wahala, amma sun zama wajibi domin ci gaban ƙasar.
Ya kuma yi kira ga masu ra’ayin ci gaba a faɗin Najeriya da su haɗa kai wajen marawa Tinubu baya, yana mai cewa wa’adin mulki na biyu zai taimaka wajen hanzarta sauye-sauyen tattalin arziki da samar da wadata ga ’yan Najeriya.
Soludo ya jaddada cewa APGA za ta ci gaba da kasancewa abokiyar tafiyar Tinubu a siyasa da shugabanci.



