
Tsohon kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na Jihar Kano, Injiniya Mansur Ahmed, ya yi murabus daga jam’iyyar APC, yana mai cewa ya damu da yadda al’amuran jam’iyyar ke tafiyar hawainiya.
Mansur, wanda ke da kusancin siyasa da tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da ficewarsa ne cikin wata wasiƙar murabus da ya miƙa wa shugaban APC na mazabar Yakasai da ke ƙaramar hukumar Kano Municipal.
Matakin nasa ya zo ne kasa da mako guda bayan wani fitaccen ɗan siyasa a jihar, Architect Aminu Dabo, tsohon Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), shi ma ya fice daga jam’iyyar.
A cikin wasiƙar, Ahmed ya ce ya ɗauki matakin ne bayan nazarin halin da jam’iyyar ke ciki tare da abokan siyasarsa.
Ya bayyana cewa wannan yanayi, tare da buƙatar bayar da gudummawa mai ma’ana wajen ci gaban Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya, sun sa ya yanke shawarar neman wata jam’iyyar siyasa da zai koma.
Ya ce akwai buƙatar samun dandalin siyasa da zai ba da fifiko ga kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da inganta jin daɗin ’yan ƙasa.
Sai dai tsohon kwamishinan ya gode wa shugabanni, masu ruwa da tsaki da mambobin APC, musamman na Kano Municipal, bisa damar da suka ba shi ta yi wa jam’iyyar hidima da kuma bayar da gudummawa wajen bunƙasarta.
Mansur Ahmed ya riƙe muƙamin kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, daga shekarar 1999 zuwa 2003.
Ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da kuma Jami’ar Bradford da ke Ingila.
Haka kuma, injiniyan ya taɓa neman takarar gwamnan Kano, sannan ya riƙe muƙamin mataimakin mai tsara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Goodluck Jonathan da Namadi Sambo a jihar Kano.



