
Wata babbar kotun Jihar Kano ta yanke wa Ayuba Sani Tumfafi hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru 10 bisa samunsa da laifin kashe abokinsa, Ibrahim Dan Larai, bayan wata sa-in-sa da ta shiga tsakaninsu kan farkar da shi domin sallar Asuba kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Mai shari’a Dije Abdu Aboki, wadda ta jagoranci shari’ar a Babbar Kotun mai lamba 1, ce ta yanke hukuncin bayan sauraron shaidu da kuma bayanan bangarorin biyu.
Bayanai daga shari’ar sun nuna cewa rikici ya barke tsakanin Tumfafi da marigayin kan batun farkar da shi domin gudanar da sallar Asuba, wanda daga bisani ya kai ga mutuwar Ibrahim.
Lauyar masu gabatar da kara, Amina Uba Adamu, ta gabatar da shaidu uku da kuma wasu hujjoji guda uku a gaban kotun, yayin da Tumfafi ya kare kansa daga zargin da ake masa.
Bayan kotun ta same shi da laifin kisan kai ba bisa ka’ida ba, ta yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru 10.
Haka kuma, kotun ta umarce shi da ya ci gaba da neman ilimin addinin Musulunci da na boko yayin da yake zaman gidan gyaran halin.



