
Hukumar kula da cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) ta kunna cibiyar ayyukan gaggawa ta lafiya domin shirin tunkarar cutar Ebola, bayan gwamnatin tarayya ta tabbatar da bullar cutar a Abuja.
Daraktan hukumar, Farfesa Muhammad Adamu-Abbas, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce Kano na cikin shirin ko-ta-kwana.
Ya ce an killace wanda ya kamu da cutar a Abuja, yayin da ake sanya ido kan mutum 44 da suka yi mu’amala ta kusa da shi.
Daraktan ya bukaci mazauna Kano su kwantar da hankalinsu, amma su kiyaye dokokin kariya, ciki har da guje wa shan magani da kansu da kuma kai rahoton duk wanda ya nuna alamun cutar ga jami’an lafiya.
Alamomin Ebola sun hada da zazzabi mai tsanani, kasala, matsanancin ciwon kai, ciwon gabobi, amai, gudawa, ciwon ciki da zubar jini ba tare da wani dalili ba.
Ya kuma shawarci jama’a su rika wanke hannayensu da sabulu da ruwa mai gudana, su guji taba jinin ko ruwan jikin wanda ya kamu da cutar, kayansa ko gawarsa, tare da guje wa cin naman daji.
Hukumar ta bukaci duk wanda ke da zazzabi tare da wasu alamomin cutar, musamman wanda ya yi tafiya ko mu’amala da mara lafiya, da ya tuntubi jami’an lafiya nan take.
An bukaci jama’a su kira 07077974504 ko su tuntubi jami’an sa ido kan cututtuka a kananan hukumominsu domin samun taimako.
Haka kuma, hukumar ta umarci asibitocin gwamnati, masu zaman kansu, na addini da na sojoji da su kara sa ido tare da bin ka’idojin hana yaduwar cututtuka domin kare marasa lafiya da ma’aikatan lafiya.



