By Muhammad Sani Muazu

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi sunayen mutane shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin naɗa su a matsayin kwamishinoni da mambobin majalisar zartarwa ta jihar.
Kakakin majalisar, Jibril Ismail Falgore, ne ya karanta wasiƙar gwamnan yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Waɗanda aka miƙa sunayensu sun haɗa da Air Commodore Salisu Yusha’u mai ritaya, Farfesa Sani Lawan da Hon. Muntari Ishaq.
Sauran sun haɗa da Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, Hon. Idris Garba Mustapha da Ibrahim Namadi Dala.
Ana sa ran majalisar za ta gudanar da matakan da suka dace na tantance waɗanda aka zaɓa kafin kammala shirin naɗa su.



