Home / Latest / An Kwantar Da Ɗalibai Fiye Da 100 Na Ɗalibai A Asibiti Bayan Shakar Iskar Gas A Ogun

An Kwantar Da Ɗalibai Fiye Da 100 Na Ɗalibai A Asibiti Bayan Shakar Iskar Gas A Ogun

Sama da ɗalibai 100 a wasu makarantun sakandare a garuruwan Ijebu Ode, Ago Iwoye da Ijebu Igbo, a Jihar Ogun, sun kwanta asibiti bayan sun shaki wata iska mai guba.

An garzaya da ɗaliban zuwa asibitocin gwamnati da sauran cibiyoyin lafiya, ciki har da Asibitin Jiha da ke Ijebu Ode da Babban Asibitin Ijebu Igbo, bayan wasu daga cikinsu sun suma tare da fuskantar matsalar numfashi.

Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa makarantun da lamarin ya fi shafa sun haɗa da Ijebu Igbo Girls Grammar School, Anglican Girls Grammar School da ke Ijebu Ode, da kuma Itamerin Comprehensive High School da ke Ago Iwoye.

Wani malami a ɗaya daga cikin makarantun da abin ya shafa ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10 na safiyar Laraba, inda wasu ɗalibai da ma’aikata suka fara fama da matsalar numfashi tare da suma.

Ya ce wasu makarantu a Ago Iwoye sun rufe da misalin ƙarfe 11 na safe saboda tsanantar lamarin, yayin da wasu iyaye suka garzaya makarantu domin ɗaukar yaransu.

Wannan dai shi ne karo na huɗu da irin wannan matsala ta faru a yankin tun watan Afrilun 2026, inda a baya ɗalibai kusan 40 suka kamu, sannan sama da 120 suka kwanta asibiti a watan Mayu, yayin da wasu 69 suka kamu a ranar 1 ga Yuni.

A nasa ɓangaren, Kehinde Bello, mai taimaka wa Gwamnan Ogun kuma babban manajan hukumar kula da muhalli ta jihar, ya ce bincike ya nuna cewa iskar na iya fitowa daga ƙarƙashin ƙasa sakamakon yanayin ƙasa da layukan karkacewar duwatsu, ba wai fashewar bututun iskar gas ko wani aikin zagon ƙasa ba.

Ya ce gwamnati na ƙoƙarin samo mafita ta dindindin, tare da tabbatar da cewa ana ba ɗaliban da abin ya shafa kulawar lafiya.