
Majalisar Wakilai ta Tarayya na nazarin wani kudirin doka da ke neman hana masu gidaje, kamfanonin kula da kadarori da dillalan gidaje karɓar kuɗin haya na sama da watanni 12 a Abuja.
Kudirin, wanda ’yan majalisa Paul Nnamchi mai wakiltar mazabar Enugu East/Isi-Uzo da Ahmed Doro mai wakiltar Bindawa/Mani a Jihar Katsina suka gabatar, na neman kafa hukumar da za ta kula da harkokin haya da kare haƙƙin ’yan haya.
Kudirin ya kuma tanadi hana masu gidaje kauce wa dokar ta hanyar amfani da dillalai, ƙarin kuɗaɗen hidima ko wasu yarjejeniyoyi da za su tilasta wa ’yan haya biyan kuɗin haya na sama da shekara guda a gaba.
Sai dai kudirin ya amince wa ɗan haya ya biya kuɗin haya na sama da shekara guda idan shi da kansa ya nemi yin hakan ba tare da tilastawa, barazana, nuna wariya ko ramuwar gayya ba, kuma aka rubuta yarjejeniyar.
Haka kuma, kudirin ya tanadi cewa masu gidaje ko wakilansu su riƙa bai wa ’yan haya yarjejeniyar haya a rubuce, wadda za ta bayyana kuɗin haya, lokacin biyan sa, tsawon zaman haya, kuɗin ajiya da sauran haƙƙoƙi da nauyin da ke kan ɓangarorin biyu.
Idan aka amince da kudirin, za a kafa Hukumar Kula da Dokokin Haya da Kare ’Yan Haya ta Abuja (FCT Rent Regulation and Tenants’ Protection Authority), wadda za ta binciki koke-koke, sa ido kan bin doka da sasanta rikice-rikicen haya.
Hukumar za ta kuma iya umartar mai gida ya mayar wa ɗan haya kuɗin da ya karɓa ba bisa ƙa’ida ba cikin kwanaki 30 bayan an miƙa masa umarnin.
Kudirin ya tanadi tarar kuɗi daga naira 500,000 zuwa naira miliyan biyar ga mutanen da aka samu da laifin karya dokar karɓar kuɗin haya na gaba, yayin da kamfanoni za su fuskanci tarar naira miliyan biyar zuwa miliyan 20.
Haka kuma, duk wanda ya ƙi bin sahihin umarnin hukumar na gyara saɓa wa doka, zai iya fuskantar tarar da ba ta wuce naira miliyan ɗaya ba.
Kudirin ya kuma bai wa masu gidaje da ’yan haya damar neman adalci a kotu, inda duk wanda bai gamsu da hukuncin hukumar ba zai iya ɗaukaka ƙara zuwa Babbar Kotun Abuja cikin kwanaki 30.
A shekarar da ta gabata, majalisar ta gabatar da shawarar takaita ƙarin kuɗin haya a faɗin ƙasar zuwa kashi 20 cikin 100, tare da buƙatar gwamnatin tarayya ta tabbatar da aiwatar da matakin. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da aiwatar da shawarar ba.



