
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba zai halarci dukkan tarukan kamfen jam’iyyar APC ba gabanin zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa dole ne ya ba da fifiko ga gudanar da mulki, tattalin arziki da jawo masu zuba jari zuwa ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026, yayin ƙaddamar da kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC a Abuja, inda ya buƙaci mambobin kwamitin su jagoranci yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a faɗin ƙasar.
Shugaban ƙasar ya ce ya amince da shawarar cewa harkokin kamfen bai kamata su hana shi gudanar da ayyukan gwamnati ba, saboda Najeriya na buƙatar kulawarsa a halin yanzu.
Ya bayyana cewa ba zai iya halartar dukkan tarukan kamfen ba saboda akwai muhimman ayyukan gwamnati da suka haɗa da biyan basussuka da sauran nauyin kuɗi da ƙasar ke fuskanta, ciki har da bashin da ake bin Najeriya daga Amurka.
Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin jawo masu zuba jari waɗanda za su kafa kasuwanci mai ɗorewa tare da taimakawa ci gaban tattalin arzikin Najeriya da samar da kyakkyawar makoma ga al’ummar ƙasar.
Duk da cewa ba zai halarci dukkan tarukan kamfen ba, shugaban ƙasar ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa zai ware lokaci domin yin magana da su kai tsaye, yayin da kwamitin ke gudanar da ayyukan kamfen a jihohi da ƙananan hukumomi.
A ƙarshe, Tinubu ya bayyana ƙaddamar da kwamitin a matsayin wani sabon alƙawari ga al’ummar Najeriya, yana mai bayyana kwarin gwiwarsa kan nasarar APC a zaɓen 2027. Ya kuma buƙaci mambobin kwamitin su tabbatar da samun ƙuri’u a mazabunsu, domin a cewarsa, ba za a yaba musu ba sai sun kammala wannan aiki.



