
Mata uku ne rak a ƴan takara 251 da ke neman kujerar majalisar wakilai a jam’iyyu daban-daban gabanin zaɓen 2027 a jihar Kano.
Wani rahoto da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya wallafa ta nuna cewa INEC ce ta fitar da jerin sunayen na ƙarshe wanda Sakatariyar hukumar ta ƙasa, Rose Oriaran-Anthony ta sanya wa hannu.
Jerin sunayen ya nuna cewa maza sun mamaye sunayen ƴan takarar, inda ’yan takara 248 suka fito neman kujeru 24 da ake da su a mazabun tarayya na jihar.
Ɗaya daga cikin matan da ke takarar ita ce Aisha Abba-Mahmud, mai shekara 28, wadda ke neman kujerar mazabar tarayya ta Dala a ƙarƙashin jam’iyyar National Rescue Movement (NRM).
Halima Ahmad, mai shekara 58, na neman kujerar mazabar tarayya ta Gwale a ƙarƙashin jam’iyyar African Action Congress (AAC), yayin da Binta Ahmad, mai shekara 27, ke neman kujerar mazabar tarayya ta Nasarawa a ƙarƙashin jam’iyyar Action Democratic Party (ADP).
Haka kuma, mata biyu ne kawai ke takarar kujerun Sanatoci a jihar da su ka haɗa da Rabi Aliyu ta jam’iyyar AAC, wadda ke neman kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya, da kuma Jamila Muhammed ta jam’iyyar National Democratic Party (NDP), wadda ke neman kujerar Sanatan Kano ta Arewa.
Ƙarancin matan da ke takara ya nuna babban gibi tsakanin maza da mata a Jihar Kano wajen neman kujerun Majalisar Dokoki ta Ƙasa, wato Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa.



