Home / Politics / Ba Domin Mu Riƙa Juya Yakubu Adamu Za Mu Kawo Shi A Matsayin Gwamna Ba – Bala Mohammed

Ba Domin Mu Riƙa Juya Yakubu Adamu Za Mu Kawo Shi A Matsayin Gwamna Ba – Bala Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana cewa goyon bayan kawo Dr. Yakubu Adamu a matsayin gwamnan jihar a zaɓen 2027 ba wai don a riƙa juya shi ba ne, sai dai domin ci gaban jihar Bauchi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban asusun TETFund, Farfesa Suleiman Bogoro, a garin Gwarangah da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro.

Bala Mohammed ya bayyana Yakubu Adamu a matsayin mutumin da ba ya cikin Fulani masu zaman banza, yana mai nuna cewa yana da ƙwazo da hangen nesa wajen gudanar da al’amura.

Haka kuma, gwamnan ya ja kunnen al’ummar jihar Bauchi da kada su zaɓi mutanen da yake zargi da alaƙa da masu garkuwa da mutane, yana mai jaddada muhimmancin tsaro da zaɓen shugabannin da za su yi aiki domin ci gaban jihar.

Tagged: