Home / Latest / Gwamnatin Tinubu na aiwatar da ayyukan more rayuwa na Tiriliyan 9.5 a Kano – Abba

Gwamnatin Tinubu na aiwatar da ayyukan more rayuwa na Tiriliyan 9.5 a Kano – Abba

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce Gwamnatin Tarayya na aiwatar da ayyukan more rayuwa da suka haura naira tiriliyan 9.5 a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da wani muhimmin sashe na babbar hanyar Abuja–Kaduna–Zariya–Kano, inda ya wakilci Shugaba Tinubu.

Ya ce ayyukan sun haɗa da gine-ginen hanyoyi, layin dogo da sauran manyan ayyukan raya ƙasa da nufin bunƙasa tattalin arziki.

Abba ya bayyana cewa babbar hanyar za ta sauƙaƙa zirga-zirga, rage lokacin tafiya da haɗurran hanya, tare da inganta jigilar kayayyakin gona da na kasuwanci a Arewacin Najeriya.

Ya lissafa wasu ayyukan gwamnatin tarayya a Kano da suka haɗa da hanyar Kano–Kaduna, Kano–Maiduguri, Kano Northern Bypass, Kano–Katsina, layin dogo na Kano–Katsina–Maradi da bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano.

Gwamnan ya kuma roƙi gwamnatin tarayya ta taimaka wajen gyaran hanyoyin Eastern da Western Bypasses da sauran manyan hanyoyin da ke haɗa ƙauyuka a jihar.

Ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya domin hanzarta ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar al’ummar Kano.

A nasa jawabin, Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ce an kammala kilomita 118 na babbar hanyar Abuja–Kaduna–Zariya–Kano ta amfani da fasahar shimfiɗa kankare.

Ya bayyana cewa an kammala sashe na farko mai tsawon kilomita 252 kan kuɗi kusan naira biliyan 252.118, yayin da aka kammala kilomita 148 daga cikin 164 na sashe na biyu.

Umahi ya ce gwamnatin Tinubu ta umurci ma’aikatar ayyuka da ta nemo hanyoyin kammala aikin bayan ɗan kwangilar farko ya kasa samun kayan aikin da ake buƙata.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin tsawaita sashen hanyar da ke Kano har zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.