By Muhammad Sani Muazu

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci dan majalisa mai wakiltar Nassarawa, Yusuf Bello-Aliyu, domin ya bayyana kan wasu kalamai da yin bidiyon daga kunnuwan zomo da ake zargin ya yi, wadanda suka bazu a kafafen sada zumunta.
Kakakin majalisar, Jibril Ismail-Falgore, ne ya sanar da matakin yayin zaman majalisar ranar Litinin, bayan kudirin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar Minjibir, Abdulhamid Abdul-Minjibir, ya gabatar.
Abdul-Minjibir ya ce ya ga wani rubutu da Bello-Aliyu ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda yake rike da kunnuwan zomo tare da furta kalaman da ya bayyana a matsayin wadanda ba su dace da matsayin dan majalisa ba.
Ya bukaci a mika lamarin ga kwamitin ladabtarwa na majalisa domin gayyatar dan majalisar ya yi bayani kan dalilin aikata hakan.
Shi ma Musa Ali-Kachako, mai wakiltar Takai, ya bukaci majalisar ta dauki matakin ladabtarwa bisa dokokinta, yana mai cewa ya kamata ‘yan majalisa su zama abin koyi ga al’umma.
A nasa bangaren, Usman Abubakar-Tasiu, mai wakiltar Kiru, ya nuna damuwa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta wajen cin zarafi da zagin mutane, tare da bukatar samar da doka domin daidaita amfani da su.
Daga bisani, Kakakin majalisar ya mika batun ga kwamitin ladubban majalisar, wanda zai gayyaci Bello-Aliyu domin ya bayyana a gabansa ranar Talata.



