Home / Latest / Wike ya soki Obi kan ziyartar sansanonin ’yan gudun hijira

Wike ya soki Obi kan ziyartar sansanonin ’yan gudun hijira

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya soki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, kan yawan ziyartar sansanonin ’yan gudun hijira a faɗin Najeriya, yana tambayar irin tawali’un da yake nunawa.

Wike ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wajen bikin karrama wasu fitattun ’yan kabilar Idoma, da aka gudanar a Abuja, inda ya yi gargaɗin cewa ’yan Najeriya su yi hattara da ’yan siyasar da ya kira masu caca gabanin zaɓen 2027.

Ministan ya tambayi dalilin da zai sa Obi, wanda bai yi bikin ranar haihuwarsa a sansanin ’yan gudun hijira ba lokacin da yake gwamnan jihar Anambra, yake ziyartar irin waɗannan sansanoni a yanzu da yake neman shugabancin ƙasa.

“Yan siyasa suna iya yin ƙarya. Mutumin da bai yi bikin ranar haihuwarsa a sansanin ’yan gudun hijira ba lokacin da yake gwamna, yanzu yana son yin hakan yana neman zama shugaban ƙasa. Sai ku ce yana da tawali’u. Wane irin tawali’u ne wannan?” Wike ya tambaya.

Obi ya bayyana a ranar 30 ga Satumba cewa ya ziyarci sansanonin ’yan gudun hijira guda 12 a Najeriya cikin ’yan makonnin baya-bayan nan, inda ya kuma buƙaci gwamnati ta inganta rayuwar mutanen da ke sansanonin.

Haka kuma, Wike ya soki ’yan siyasar da yake zargi da nuna halin taimakon jama’a a bainar jama’a domin neman farin jini, ciki har da sayen gasasshen masara da gyada a kan hanya.

Ya ce bai kamata ’yan Najeriya su yarda da irin waɗannan abubuwa su rinjaye tunaninsu ba, yana mai kare ƙoƙarin gwamnatin tarayya na magance matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Wike ya buƙaci ’yan Najeriya su kwatanta halin da ƙasar ke ciki a yanzu da yadda take a baya, domin tantance ƙoƙarin da ake yi na inganta lamura.