Home / Latest / Ƴan bindiga sun kashe jami’in immigration tare da Jikkata wani a jihar Neja

Ƴan bindiga sun kashe jami’in immigration tare da Jikkata wani a jihar Neja

Hukumar Kula da Shige da fice ta ƙasa, ta ce wasu ’yan bindiga sun kai hari kan jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya a Tunga Taya-Woro da ke Jihar Neja, inda suka kashe jami’i ɗaya tare da jikkata wani.

Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, DCI Akinsola Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis, 15 ga Oktoban 2026.

Ya ce, Harin ya faru a ranar Talata, 6 ga Oktoban 2026, da misalin ƙarfe 11:30 na safe, lokacin da jami’an biyu na ofishin Wawa suke gudanar da sintiri a yankin.

Sanarwar ta ce, Jami’in da aka kashe shi ne ASI I.U. Babangida, yayin da Inspector A.K. Musa ya samu munanan raunuka, amma ya tsere kuma yana samun kulawar likitoci. An kuma binne jami’in da ya rasu bisa tsarin addinin Musulunci.

Hukumar ta bayyana cewa tana haɗa kai da Gwamnatin Jihar Neja da sauran hukumomin tsaro domin gano waɗanda suka kai harin, kama su da gurfanar da su a gaban kotu.

Arewa Updates.