By Muhammad Sani Muazu

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya ce an kammala aikin tsara dokar kafa tsarin ’yan sanda na jihohi da kaso 90 cikin 100, kuma ana sa ran miƙa ta ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa cikin makonni biyu.
Gbajabiamila, wanda ke jagorantar kwamitin shugaban ƙasa kan sake fasalin aikin ’yan sanda, ya bayyana hakan ne bayan wani taron kwamitin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis.
Ya ce ana buƙatar ƙarin zama guda domin kammala duba wasu muhimman batutuwa, yana mai cewa gwamnoni sun gabatar da wasu ƴan shawarwari da za a yi la’akari da su.
Ya bayyana dokar a matsayin mafi muhimmanci da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gabatar zuwa yanzu, inda ya ce akwai matsaya ta bai ɗaya a ƙasa kan buƙatar gyaran kundin tsarin mulki domin kafa ’yan sandan jihohi.
Tarin ya samu halartar Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq, da gwamnonin Ogun, Dapo Abiodun, da Kaduna, Uba Sani, tare da Sufeto-Janar na ’yansanda, Tunji Disu.
Shugaba Tinubu ne ya ƙaddamar da kwamitin a watan Yulin 2026 domin tsara dokokin da za su jagoranci kafa ’yansandan jihohi.
A halin yanzu, Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta aika da kudirin gyaran kundin tsarin mulki kan kafa ’yansandan jihohi zuwa majalisun dokokin jihohi 36 domin nazari da amincewa.
Dokar da ake shirin miƙawa za ta fayyace tsarin ɗaukar ma’aikata, horarwa, samar da kuɗaɗe, sa ido da kuma haɗin gwiwa tsakanin ’yan sandan tarayya da na jihohi.



