Home / Latest / Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudirin Kafa Kwalejin Noma A Borno

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudirin Kafa Kwalejin Noma A Borno

By Muhammad Sani Muazu,

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudirin Kafa Kwalejin Noma A Borno

Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da kudirin kafa Kwalejin Noma ta Tarayya a karamar hukumar Shani da ke jihar Borno, a wani mataki na bunƙasa harkokin noma da inganta amfani da dabarun zamani wajen noma.

Kafar People’s Lens Media ta ruwaito cewa majalisar ta amince da kudirin a karatu na uku yayin zamanta na ranar Alhamis, bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar mai kula da kwalejojin noma da cibiyoyi.

Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ne ya dauki nauyin kudirin, inda ya bayyana cewa kafa kwalejin zai taimaka wajen inganta ilimin noma da rage dogaro da tsofaffin hanyoyin noma.

Ndume ya ce har yanzu Najeriya ba ta samu ci gaba sosai wajen amfani da fasahar zamani domin sauƙaƙa noma da haɓaka yawan amfanin gona ba