Home / Latest / Dattijo Tanko Yakasai mai shekara 100 ya yi wa Tinubu fatan nasara a 2027

Dattijo Tanko Yakasai mai shekara 100 ya yi wa Tinubu fatan nasara a 2027

Dattijon siyasa, Alhaji Tanko Yakasai, ya yi wa Shugaba Bola Tinubu fatan samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Yakasai, wanda ya ce an haife shi a shekarar 1925, ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Abuja.

Dattijon ya gode wa Tinubu da shugabannin APC bisa gayyatar da suka yi masa, yana mai cewa taron ya ba shi damar sake haɗuwa da tsofaffin abokan siyasa.

Ya ce, “Ina kuma son isar da saƙon fatan alheri ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da yi masa fatan samun nasara a zaɓe mai zuwa.”

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Tinubu zai yi nasara a zaɓen 2027, tare da alƙawarin jagorantar yunƙurin yaƙin neman zaɓensa.

Adeleke ya buƙaci ’yan Najeriya su ƙara ba Tinubu lokaci domin manufofinsa su fara haifar da sakamako, duk da cewa ya amince matakan ba su kasance masu sauƙi ba.

Ya ce ya shiga yaƙin neman zaɓen ne domin ganin an ɗauki matakai na zahiri, maimakon yawan magana kawai.